Isa ga babban shafi
Iran-Makamai

Muna da 'yancin iya baje kolin makaman da muka mallaka ga Duniya- Iran

Iran ta mayar da raddi kan Amurka game da da 'yancin baje kolin makamanta inda kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito babban jami'i a ma'aikatar wajen kasar na cewa babu wata doka da ta hana Tehran iya bajekolin nau'ikan makaman da ta mallaka manya da kanana.

Wasu nau'ikan makamai mallakin Iran.
Wasu nau'ikan makamai mallakin Iran. AP - Vahid Salemi
Talla

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa su na da 'yancin baje kolin makamansu, kalaman da ke zuwa bayan da Amurka ta soki lamirin kasar bisa bayyana kayan yakin da ta mallaka a shirin baje kolin makaman da ya gudana a Qatar.

Sai dai yayin zantawar Khatibzadeh da manema labarai a Tehran, ya ce Amurka ba ta da hurumin hana Iran bayyana irin karfin sojin da ta ke da shi gaban duniya.

A cewar Saeed Khatibzadeh ko shakka babu Iran na da matsayi kamar kowace kasa a duniya, wanda ke nuna itama ta na da 'yancin inganta karfin tsaronta ko kuma nuna nau'ikan wadannan kayayyaki a cikin kasashen da ke makwabta da ita.

Amurka dai ta yi kakkausar suka kan matakin na Iran a kokarin bajekolin karfin sojinta gaban Duniya yayin bikin bajekolin makaman na Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.