Ana daf da farfado da tattaunawar yarjejeniyar nukuliyar Iran
A jiya Asabar Iran da hukumar kula da makamashin nukkiliya ta duniya suka ce sun amince su bi hanyoyin warware matsalolin da ke wa yarjejeniyar nukiliyar 2015 kafar ungulu.
Wallafawa ranar:
Sanarwar na zuwa ne bayan da Rasha ta ce za ta nemi tabbaci daga Amurka kafin ta goyi bayan yarjejeniyar, lamarin da ke bada kwarin gwiwar cewa za a cimma yarjejeniya.
Shugaban hukumar makamashin nukiliyar, Rafael Grossi ya ce akwai ababe da dama da ya kamata a warware, amma hukumar ta yanke shawarar yin mai yiwuwa.
Shugaban hukumar makamashin nukiliya a Iran, Mohammed Eslami ya ce lallai bangarorin biyu sun cimma matsayar cewa za su yi musayar wasu kundaye a tsakaninsu nan da 22 ga watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu