Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Kungiyoyin mata za su fita zanga-zangar adawa da hana mata karatu a Afghanistan

Kungiyoyin da ke gwagwarmayar kwato hakkin mata a Afghanistan sun yi barazanar shirya zanga-zanga a kasar, matukar gwamnatin Taliban ta gaza bude makarantun mata, cikin wa’adin mako guda da suka bata.

Matakin Taliban na hana Mata karatu ya fusata jama'a a sassan duniya musamman kungiyoyin da ke kare hakkin matan.
Matakin Taliban na hana Mata karatu ya fusata jama'a a sassan duniya musamman kungiyoyin da ke kare hakkin matan. AP - Mohammed Shoaib Amin
Talla

Dubban makarantun sakandaren mata ne gwamnatin Taliban ta kulle, sa’oi kalilan bayan bayar da umarnin bude su duk da cewa makarantun maza sun koma aiki gadan gadan bayan kasancewarsu a rufe tsawon lokaci tun bayan kwace ikon ragamar kasar da kungiyar ta yi a watan Agustan bara.

A cewar guda daga cikin masu shirin shirya zanga-zangar Halima Nasari ta cikin wata sanarwa da ta karanta ta ce suna bukatar tallafin kasashen ketare kan yunkurin nasu tana mai cewa baza su lamunci jahilci mata a cikin kasar ba.

Jami'ar ta bayyana cewa, ko dai mahukuntan Afghanistan su amince da bude makarantun mata nan da mako guda ko kuma su tsunduma zanga-zangar kalubalantar matakin.

Halima Nasari ta bayyana cewa maimakon matakin Taliban na kulle makarantun matan kamata ya yi da ce sun samar da wani tsarin gina sabbin makarun mata zalla tare da gindaya sharuddan da suke son abi.

Batun hana ‘ya’ya mata zuwa makaranta a Afghnistan ya saba da alkawarin da gwamnatin Taliban ta dauka na sauya yadda ta tafiyar da mulkin kasar tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.