Isa ga babban shafi
Taron China

Kasashe duniya sun sha alwashin magance matsalar lalacewar muhalli

Kusan kasashe 200 sun sha alwashin magance matsalar lalacewar muhalli a wani muhimmin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a China, amma masu fafutukar kare muhalli sun soki shawarar da cewa ba ta da ma'ana domin kuwa ba zata kawo mafita ba.

Gurbatatcen iska mai lalata muhalli
Gurbatatcen iska mai lalata muhalli Hector RETAMAL AFP/Archivos
Talla

Wakilai daga wasu kasashe 195 sun ce za su goyi bayan yarjejeniyar da aka cimma a taron na China, musamman ma batun yadda za a magance batutuwan da suka shafi rayayyun halittu da basu kariya a taron da ya gudana a birnin Kunmin da ke kudancin China.

Ana sa ran yarjejeniyar da aka cimma zata kasance wani babban al’amari da zai taimaka matuka wajen cimma manufofin da aka sanya gaba a shekara mai zuwa wacce za ta fitar da tsare -tsaren kiyaye muhalli na duniya da ake fatan cimmawa a shekarar 2030 da 2050.

Duk da haka, masana muhallin sun ce shawarwarin da aka gabatar a taron basu samar da isasshen ci gaba ba kan makasudin rabe -raben halittu da kasashe suka cimma a cikin yarjejeniyar Aichi ta 2010.

A cewar rahotanni, kasashe za su ci gaba da tattaunawa kan yadda za a inganta shirin kare halittun na duniya a taron farko da za a yi a Geneva, cikin shekarar 2022, sannan daga baya a kashi na biyu na taron a watan Afrilu da Mayu da za ayi a 2023 shima za a duba hanyoyin da suka kamata a bi.

Sanarwar ta bukaci kasashe da su fahimci mahimmancin rayukan halittu, karfafa dokokin kare jinsuna, inganta shirin rabon albarkatun kwayoyin halitta, tare da wayar da kan al’umma kan yadda za su kiyaye, wajen bawa halittun doron kasa kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.