Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin bama bamai ya kashe mutane tare da jikkata da dama a Afghanistan

Mutane 2 sun mutu a Afghanistan, sakamakon fashewar wasu bama-bamai uku a birnin Jalalabad a ranar Asabar.

'Yan Afganistan a wajen Asibitin Musamman na Yankin Nangarhar bayan fashewar bama bamai a birnin Jalalabad, ranar 18 ga Satumba, 2021.
'Yan Afganistan a wajen Asibitin Musamman na Yankin Nangarhar bayan fashewar bama bamai a birnin Jalalabad, ranar 18 ga Satumba, 2021. © AFP
Talla

Harin dai shi ne irin sa na farko da aka kai a Afghanistan bayan sake karbe mulkin kasar da kungiyar Taliban ta yi a watan Agusta.

Bayanai sun ce akwai mata da kananan yara a cikin mutane akalla 18 da suka jikkata a harin bama baman.

Jalalabad shi ne babban birnin Nangarhar, in da kuma ke zama yankin da kungiyar IS reshen Afghanistan ke da karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.