Isa ga babban shafi
Afghanistan - Amurka

Za mu karkare janye dakarunmu daga Afghanistan a karshen Agusta - Amurka

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce za a karkare janye dakarun kasar daga Afghanistan a karshen watan Agusta.

Wasu sojojin kasar Amurka a birnin Kabul dake Afghanistan.
Wasu sojojin kasar Amurka a birnin Kabul dake Afghanistan. AP - Rahmat Gul
Talla

Fadar ta White House ta sanar da matakin ne a ranar Juma’a ta hannun sakataren yada labaranta Jen Psaki.

Kafin sauyin lokacin dai, 11 ga watan Satumban wannan shekara shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana a matsayin ranar janye ragowar dakarun kasar daga Afghanistan bayan shafe shekaru 20 suna gwabza yaki da mayakan Taliban da na Al’Qaeda.

A jiya Juma’a dukkanin dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO sun fice daga sansanin sojoji na Bagram mafi girma dake kasar ta Afghanistan, da ya taka muhimmiyar rawa a tsawon lokacin da suka shafe suna yaki a kasar tun daga shekarar 2001, bayan kai harin 11 ga watan Satumba a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.