Isa ga babban shafi
Myanmar

Hambarerriyar shugabar Myanmar Suu kyi ta ci watanni 3 karkashin daurin talala

Shugabar farar hular Myanmar da aka hambarar Aung San Suu Kyi ta cika wata na uku a karkashin umarnin da sojoji na daurin talala.

Masu zanga-zanga a Bangkok dauke da hotunan hambarerriyar shugaban Myanmar  ranar 7 ga watan Maris 2021
Masu zanga-zanga a Bangkok dauke da hotunan hambarerriyar shugaban Myanmar ranar 7 ga watan Maris 2021 Mladen Antonov AFP/Archivos
Talla

Al’ummar kasar sun fada cikin rikici tun bayan da sojoji suka hambarar da Suu Kyi dake da lambar yabo ta Nobel a wani juyin mulkin da aka yi mata ranar 1 ga watan Fabrairu, lamarin da ya kawo karshen gajeren zango na mulkin demokradiyya a Myanmar.

Sake dawo da mulkin soja ya haifar da guguwar zanga-zanga da kuma murkushe masu rajin kare demokradiyya, in da jami’an tsaro suka kashe mutane sama da 750, a cewar wata kungiyar dake sa ido a yankin.

Suki na fuskanatr tuhuma kan zarge-zarge da dama

Ana tuhumar Suu Kyi da aikata laifuka shida da suka hada da tawaye da kuma fallasa bayanan sirrin kasar ta Myanmar, yayin da aka hana ta ganawa da lauyoyinta.

Maimakon haka, ta yi wasu tarurruka na bidiyo ne kawai wadanda jami'an tsaro ke sa ido a dukkan bangarorin biyu, kamar yadda lauyoyin suka shaida wa  AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.