Isa ga babban shafi
Myanmar

Gwamnatin Sojin Myanmar ta yi wa Fursunoni afuwa saboda bikin shekarar gargajiya

Gwamnatin mulkin sojan Myanmar ta sanar da yin afuwa tare da sakin sama da fursunoni dubu 23 saboda bikin ranar hutun sabuwar shekara ta gargajiya ta Thingyan, to sai dai ba a bayyana ko sun hada da masu rajin kare demokradiyya wadanda aka tsare bayan karbe iko da sojojin suka yi a watan Fabrairu.

Motar da ke dauke da Fursunonin da sojojin Myanmar sukayi wa afuwa ranar Jumma'a 17 ga watan 202O a Myanmar
Motar da ke dauke da Fursunonin da sojojin Myanmar sukayi wa afuwa ranar Jumma'a 17 ga watan 202O a Myanmar AP - Thein Zaw
Talla

An sanar da sakin ne a kafar yada labarai ta kasa MRTV, wacce ta ce babban hafsan sojan kasar Janar Min Aung Hlaing ya yi afuwa ga fursunoni 23,047, ci harda ‘yan kasashen waje 137 da za a tasa keyarsu daga Myanmar. Ya kuma ragewa wasu wa’adin zaman kaso.

Wannan matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da hambarar da zababbiyar gwamnati Aung San Suu Kyi a ranar 1 ga watan Fabrairu, inda ake amfani da muggan makamai a kansu don mukushe su.

Yanzu haka adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar adawa da sojojin Myanmar ya haura 700, a daidai lokacin da bam ya tashi a Mandalay birni na biyu mafi girma a kasar a karshen makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.