Isa ga babban shafi
Myanmar

Kungiyoyi sun yi Allah wadai da zartas da hukuncin kisa a Myanmar

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya ta yi Allah wadai da gwamnatin Myanmar, kan yanke wa mutane 19 hukuncin kisa, wanda shine na farko da aka gani tun bayan da sojoji suka kwace mulki.

Masu zanga-zanga a Myanmar ranar 7 ga watan Afrelu 2021.
Masu zanga-zanga a Myanmar ranar 7 ga watan Afrelu 2021. via REUTERS - REUTERS
Talla

Myammar ta fada cikin rikici tun bayan hambarar da shugabar farar hula Aung San Suu Kyi a ranar 1 ga watan Fabrairu, inda jami’an tsaro suka kashe mutane sama da 600 yayin da masu zanga-zangar suka ki mika wuya ga shugabannin dake mulkin soja.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa, ranar Juma’a wata kotun soji ta yanke wa mutane 19 hukuncin kisa saboda samun su da laifin fashi da makami.

Kasashen duniya sun caccaki matakin kisan masu zanga-zanga a Myanmar

Ministocin tsaro na kasashe da dama sun yi tir da matakin kisan masu zanga –zanga a Myanmar a inda lokacin da suka kashe kimanin mutane 90, cikinsu har da yara bayan da jami’an tsaro suka bude musu wuta.

Sabuwar  gwamnatin sojin da ta kwace mulki da bakin bindiga, ta yi amfani da karfi fiye da kima a ranar da ta gudanar da bikin tunawa da sojojinta, a yayin da yawan wadanda suka mutu tun bayan juyin mulkin 1 ga watan Fabrairu ya haura akalla 423, a cewar kungiyoyi masu sanya ido a kan abin da ke gudana a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.