Isa ga babban shafi

Mutane 26 sun mutu a harin da aka kaiwa filin jiragen saman Yemen

Akalla mutane 26 suka aka tabbatar sun mutu, yayin da wasu gwammai suka jikkata a Yemen, sakamakon tagwayen fashe-fashen da ake kyautata zaton bama bamai ne a filin jiragen sama na Aden, babban birnin kasar.

Yadda hayaki ya turnuke yankin filin jiragen saman birnin Aden dake Yemen, bayan aukuwar tagwayen fashe-fashe dake zaton bama bamai ne
Yadda hayaki ya turnuke yankin filin jiragen saman birnin Aden dake Yemen, bayan aukuwar tagwayen fashe-fashe dake zaton bama bamai ne Reuters
Talla

Fashe-fashen sun auku a dai dai lokacin da tawagar sabuwar gwamnatin hadin kan kasar ta Yemen suka sauka a filin jirgin.

Jami’an agaji sun ce sama da mutane 50 suka jikkata, tare da bayyana fargabar hauhawar adadin wadanda tashin hankalin ya rutsa dasu, sai dai dukkanin jami’an gwamnatin da suka suka a filin jiragen sun tsira ba tare da raunuka ba.

Bayanai sun ce an samu fashewar farko a wurin da fasinjoji ke tsayuwa, ta biyu kuma a dai dai lokacin da mutane ke kokarin kaiwa wadanda fashewar farko ta rutsa dasu dauki. Har yanzu dai ba’a tantance abinda ya haddasa fashe-fashen ba, wadanda jim kadan bayan aukuwarsu aka jiyo musayar wutar rugugin manyan bindigogi.

Ranar 18 ga watan Disamban nan mai karewa, aka kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa tsakanin mayakan ‘yan aware dake kudancin Yemen da kuma gwamnatin kasar da kasashen duniya ke marawa baya, inda suka sha alwashin murkushe ‘yan tawayen Huthi da a yanzu ke iko da kusan baki dayan arewacin kasar, bayan kwace birnin San’a.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai farmakin, sai dai wasu daga cikin mukarraban gwamnatin Yemen na zargin ‘yan tawayen Huthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.