Isa ga babban shafi
Hong Kong

An sake yin arrangama tsakanin yan sanda da masu zanga-zanga

Yau lahadi Yan sanda da masu zanga-zanga sun sake yamutsa a yankin Hong Kong, lamarin da ke nuna cewa zanga-zanga da tashin hankalin da ya biyo bayan dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China basu dauko hanyar karewa ba a nan kusa.

Masu zanga-zanga sun sake fita kan titunan Hong Kong.
Masu zanga-zanga sun sake fita kan titunan Hong Kong. Philip FONG / AFP
Talla

Arrangamar ta auku ne bayan da masu zanga-zangar suka kafa shingayen karfe a yankin Shan Tin da ke kan iyakar yankin na Hong Kong da China, jami’an tsaro kuma suka yi amfani da barkonon tsohuwa gami da kulake wajen kokarin tarwatsa su.

A karshen watan da ya gabata, wani gungu daga cikin masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin zauren majalisar dokokin yankin, inda suka yi barna sosai, duk kuwa da cewa, shugabar yankin Carrie Lam ta yi sanar da yin watsi da kudirin dokar ta mika masu laifi zuwa China don fuskantar shari’a.

Tarzomar yankin na Hong Kong dai ta ja hankalin Birtaniya, wadda a shekarar 1997 ta bai yankin ‘yancin cin gashin kai bayan yi masa mulkin mallaka, inda Sakataren Harkokin wajenta, Jeremy Hunt, ya yi kira ga dukkan bangarori da su kwantar da hankalinsu.

A makwannin da suka gabata cikin wani sakon bidiyo, shugabar gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam ta caccaki masu zanga–zangar, tana mai bayyana tarzomar da ta biyo baya a matsayin wani shiryayyen al'amari,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.