Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Harin Taliban a Ofishin leken asirin Afghanistan ya kashe mutane 65

Rahotanni daga kasar Afghanistan na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu a harin da kungiyar Taliban ta yi ikirarin kai wa kan shalkwatar hukumar leken asirin kasar ya kai 65 bayan mutuwar wasu da dama da suka jikkata.

Daruruwan jami’an tsaron Afghanistan dai na ci gaba da rasa rayukansu a hannun mayakan Taliban tun bayan ficewar dakarun tsaro na NATO daga kasar a shekarar 2014.
Daruruwan jami’an tsaron Afghanistan dai na ci gaba da rasa rayukansu a hannun mayakan Taliban tun bayan ficewar dakarun tsaro na NATO daga kasar a shekarar 2014. REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Harin wanda Taliban ta kai tun da yammacin jiya Litinin a take ya hallaka mutane 12 yayinda aka kwashi wasu da dama zuwa Asibiti a cewar hukumomin kasar sai dai Mohammad Sardar mataimakin shugaban yankin Wardak ya bada tabbacin cewa sun kwashe gangar jikin mutane 65 daga jiya zuwa yau a karkashin baraguzan gine-gine.

Shi ma wani jami’in tsaro da ke ma’aikatar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya haura 70.

Tun farko dai mayakan na Taliban sun aike da dan kunar bakin wake ne kuma bayan tashin bom din da ke daure jikinsa suka isa wurin da bindigogi suka rika harbin mutanen da ke kokarin gujewa harin.

Rahotanni sun ce mutumin da ya yi kunar bakin waken a Ofishin hukumar leken asirin na sanye ne da kaya na musamman da manyan Jami’an tsraon Afghanistan ke sawa, matakin da ya bada damar bashi izinin shiga ginin ba tare da kwararan tuhume-tuhume ba.

Daruruwan jami’an tsaron Afghanistan dai na ci gaba da rasa rayukansu a hannun mayakan Taliban tun bayan ficewar dakarun tsaro na NATO daga kasar a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.