Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban-Iran

Jagororin Taliban sun isa Iran game da sulhunsu da Afghanistan

Kasar Iran ta sanar da isowar shugabannin kungiyar Taliban birnin Tehran yau Litinin a wani mataki na ci gaba da tattaunawa kan yadda za a kawo karshen yakin Afghanistan da aka shafe shekaru 17 ana yi.

Tun kafin yanzu dai Taliban ta gindaya sharadin cewa za ta amince da tattaunawar sulhu tsakaninta da Afghanistan matukar Amurka ta janye dakarunta daga kasar.
Tun kafin yanzu dai Taliban ta gindaya sharadin cewa za ta amince da tattaunawar sulhu tsakaninta da Afghanistan matukar Amurka ta janye dakarunta daga kasar. Parwiz/REUTERS
Talla

Wannan dai ne karo na biyu da jagororin kungiyar ta Taliban ke zuwa Iran don tattaunawar game da sasanta tsakaninsu da gwamnatin Afghanistan tun bayan da Iran din ta daura aniyar ganin ta shiga tsakani don sulhuntawa a wani yunkuri na kawo karshen yakin kasar da aka shafe kusan shekaru 17 ana yi.

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Bahram Ghasemi ya wasu bayanan kai tsaye da ya yi ta gidan talabijin din kasar, ya ce tun a jiya Lahdi wakilan na Taliban suka iso Iran kuma suka samu tarba daga mataimakin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi.

Ziyarar ta Taliban zuwa Iran ta zo ne kwanaki kalilan bayan makamanciyarta da Sakatarern majalisar kolin harkokin tsaron Iran Ali Shamkani ya kai Afghanistan inda ya tattauna da bangarorin biyu.

Cikin Jawaban Bahram Ghasemi ya ce Iran na daukar matakan da suka dace ne wajen ganin ta sasanta rikicin kasashen makwabtanta dama sauran kasashen gabas ta tsakiya.

Iran dai ta daura damarar ganin ta taimaka wajen sasanta rikicin kasar ne tun bayan da Amurka ta nuna yiwuwar janye ilahirin dakarunta da ke Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.