Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta arewa ta komawa shirin kera makamai masu cin dogon zango

An diga ayar tambaya dake cewa, anya shugaba Kim Jong-un na kasar Koriya ta arewa ba wasa ya ke da hankalin shugaba Donald Trump na Amruka ba? Kimanin watanni 2 da gudanar da zaman taro tsakanin shugabanin 2 a Singapour, maáikatar liken asirin kasar Amruka ta bayyana damuwarta kan shirin kwance damarar makaman nukiliyar gwamnati Pyongyang.

Shuhaban Korea ta arewa Kim Jong-un, kewaye da tsofin sojoji a wannan hoto da  gwamnatin Pyongyang ta yada a ranar  27 Yuli 2018 .
Shuhaban Korea ta arewa Kim Jong-un, kewaye da tsofin sojoji a wannan hoto da gwamnatin Pyongyang ta yada a ranar 27 Yuli 2018 . KCNA via REUTERS ATTENTION EDITORS
Talla

Maáikatar liken asirin kasar Amruka ta bayyana matukar damuwarta, inda ta ce yanzu haka kasar Koriya ta arewa na ci gaba da kera wasu sabin makamai masu linzame dake cin zangon kasa da kasa

Hukumar liken asirin ta ce, mi kera makami mai lizzame dake cin dogon zangon kilo mita dubu 5 ke nufi ? kuma ba sabon abu bane kasar Koriyar ta arewar na furta cewa, tana iya kera makamain da zai iya cin dogon zangon da zai kai ga kasar Amruka

hukumar ta Amruka ta koka ne, ganin yadda kasar ta Koriya ke ci gaba da kera irin wadannan makamai na nukiliya, kamar dai babu abin da ya faru duk da taron Singapur da aka gudanar tsakanin shuwagabanin kasashen 2, kasar ta komawa aikin kera makaman masu yawa

A makon da ya gabata ma, sai da sakataren harakokin wajen Amruka Mike Pompeo, ya fito fili ya tabbatar da cewa mahukumtan Pyongyang na ci gaba da inganta sanadaran kera makaman masu linzame, da suka hada da sanadarin uranium da plutonium.

Wanda hakan ke nuna cewa a fili yake kasar koriya ta arewa na ci gaba da inganta sanadaran da zasu kaita ga kera mugun makamain nan na kare dangi (Bombe atomiques).

Babu wani abin da ya sauya daga manufofinta, domin ta na da kayyakin samar da nukliya, kuma suna aiki kan makamai masu linzame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.