Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Moon Jae-in ya lashe zaben shugabancin Korea ta Kudu

Moon Jae-in na jam'iyyar Democrat, ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kasar Korea ta Kudu da gagarumin rinjaye, bayan shirya gudanar da zaben da ka yi, domin maye gurbin tsohuwar shugabar kasar Park Geun-Hye da aka tsige bisa zargin cin hanci da rashawa.

Moon Jae-in and Choo Mi-ae, zababben shugaban kasar Korea ta Kudu, yayin da yake gaisawa da magoya bayansa a birnin Seoul.
Moon Jae-in and Choo Mi-ae, zababben shugaban kasar Korea ta Kudu, yayin da yake gaisawa da magoya bayansa a birnin Seoul. REUTERS/Kim Kyunghoon
Talla

Mr. Moon wanda sanannen lauya ne mai kare hakkin dan’adam, kuma mai sassaucin ra'ayi ya yi wa abokan takararsa guda 13 fintikau a zaben, nasarar da ta bashi damar maye gurbin shugaba Park Guen-Hye da zargin cin hanci yayi awon gaba da kujerarta.

Sakamakon zaben da wasu manyan gidajen talabijin na Korea ta Kudun suka sanar, ya nuna cewa Moon ya samu kashi 41.4 daga cikin kuri’un da aka kada, yayinda mai biye da shi Hong Joon-Pyo ya samu kashi 23.3, sai kuma Ahn Cheol-Soo ya 21.8 na kuri’un.

Karo na farko kenan cikin shekaru 20 da suka gabata, da yawan al’ummar kasar da suka kada kuri’unsu ya kai kashi 77.2 a zaben sugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.