Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Sabuwar zanga zanga ta barke a Korea ta Kudu

Dubban al’ummar kasar Korea ta Kudu ne ke gudanar da wata sabuwar zanga-zangar neman a kama tare da iza keyar shugabar kasar Park Guen-Hye da majalisar kasar ta tsige daga mukaminta.

Dubban 'yan kasar Korea ta Kudu da ke zanga zanga a babban birnin kasar Seoul
Dubban 'yan kasar Korea ta Kudu da ke zanga zanga a babban birnin kasar Seoul ©REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

Rahotanni sun ce sama da mutane 600,000 ne ke gudanar da wannan zanga-zanga, inda suka fuskanci ginin fadar gwamnatin kasar da ofishin Firaministan kasar Hwang Kyo-ahn.

A dai ranar 9 ga watan Disamban da ya gabata Majalisar kasar Korea ta Kudu da tsige Park daga mukaminta sakamakon bankado hannunta cikin wata badakalar makudan kudade.

Kawo yanzu ana cigaba da dakon hukuncin da Kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar kan tsigewar da aka yiwa Park.

Wannan dai shi ne karo 10, da al’ummar kasar Korea ta kudu ke zanga zangar neman sauke Park daga shugabanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.