Isa ga babban shafi
Korea

Majalisar Korea ta Kudu ta tsige shugabar kasar Park Geun-Hye

‘Yan majalisun kasar Korea ta Kudu, sun gabatar da kudurin tsige shugabar kasar Park Geun-Hye, sakamakon zarginta da aikata almundahana, da kuma cin hanci da rashawa.

Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-Hye
Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-Hye
Talla

Wannan zargi dai ya kawo tsaiko ga gwamnatin Park, wanda kuma yasa dubban mutanen kasar gudanar da zanga-zanga, don neman shugabar kasar ta sauka daga mukaminta.

‘Yan majalisu 234 ne suka kada kuri’ar tsige shugabar kasar, yayinda 56 suka ki amincewa.

A halin yanzu, baki dayan ikon Park Geun-Hye ya koma ga Firaministan kasar ta Korea, Hwang Kyo-ahn, har sai kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin tabbatar da tsigewar da 'yan majalisun kasar suka yi ko akasin haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.