Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Ana zaben shugaban kasa a Korea ta Kudu

Al’ummar Korea ta Kudu na gudanar da zaben shugabancin kasa a wannan Talata don zaben wanda zai maye gurbin shugaba Park Guen Hye da aka tsige saboda zargin ta da cin hanci da rashawa.

Al'ummar Korea ta Kudu na kada kuri'u a rumfunan zabe dubu 139 da ke fadin kasar
Al'ummar Korea ta Kudu na kada kuri'u a rumfunan zabe dubu 139 da ke fadin kasar REUTERS/Kim Hongji
Talla

Ana kyautata zaton Moon Jae-in mai sassaucin ra’ayi zai fi samun yawan kuri’u fiye da Ahn Cheol mai matsakaicin ra’ayi a fafatawar da ‘yan takara 13 ke yi da juna.

Akwai yiwuwar Mr. Moon ya sauya matsayin kasar kan makwabciyarta Korea ta Arewa, in da ake ganin zai bukaci karfafa hanyoyin ganawa da ita.

Sai dai burin al’ummar kasar da ke kada kuri’un bai wuce yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta tattalin arzikin kasar ba.

Ana gudanar da zaben ne a mazabu sama da dubu 139 a fadin kasar, yayin da ake saran rufe rumfunan zaben da misalin karfe 11 agogon GMT.

Akwai yiwuwar rantsar da duk wanda ya yi nasara a zaben a gobe Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.