Isa ga babban shafi
Syria

Yawan wadanda suka mutu a harin Syria ya karu zuwa 72

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai da makami mai guba kan fararen hula a garin Khan Sheikhun a lardin Idlib na kasar Syria ya karu daga 58 zuwa 72.

Hoton Bidiyo da ke nuna yadda ake kokarin ceto ran wani da harin iskar gas mai guba ya rutsa da shi a Khan Sheikhun na lardin Idlib a Syria.
Hoton Bidiyo da ke nuna yadda ake kokarin ceto ran wani da harin iskar gas mai guba ya rutsa da shi a Khan Sheikhun na lardin Idlib a Syria. Reuters
Talla

Jami’an sa ido sun ce 20 daga cikin wadanda suka mutu kananan yara ne, yayinda 17 daga ciki mata.

A yau Laraba kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da zama na musamman, domin daukar mataki kan da harin da aka akai da iskar gas mai guba.

Kasashen Fransa da Birtaniya ne suka bukaci a gudanar da zaman domin tattaunawa kan matakan da suka dace.

Sai dai a wani sabon al’amari, kasar Rasha ta ce tabbas jiragen yakin Syria ne suka kai farmaki kan garin na Khan Sheikhun, sai dai fa ba ta hanyar amfani da makami mai guba ba.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce harin ya fada ne kan wani rumbun ajiyar ‘yan tawayen kasar da yake makare da sinadarai masu guba, da ke daf da garin na Khan Sheikhun, wanda hakan ke tabbatar da cewa 'yan tawayen kasar ne suka mallaki makaman, ko kuma sinadaran masu guba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.