Isa ga babban shafi
Philippines

Jami'an tsaron Philippines sun kama 'yar majalisar dattawa

Jami’an tsaro a kasar Philippines sun kama wata mata da tayi kaurin suna wajen sukar matakan da shugaban kasar Rodrigo Duterte ke dauka wajen yaki da masu mu’amala da miyagun kwayoyi.

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte Reuters
Talla

Leila de Lima wadda ‘yar Majalisar Dattawa ce, tace ana neman shafa mata kashin kaji ne dan ganin ta daina Magana kan kama karyar da shugaban da jami’an keyi wajen hallaka wadanda basuji basu gani ba.

Sanata de Lima ta musanta cewar ta amfana da cinikin ko kuma kudaden sayar da kwayoyin, kuma ta sha alwashin wanke kan ta.

Shugaba Duterte ya zargi Sanatan da amfana da cinikin kwayar inda yayi alkawarin murkushe ta a bainar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.