Isa ga babban shafi
Philippines

Fursunoni 150 sun tsere a Philippines

Fiye da fursunoni 150 sun tsere daga wani gidan yarin kasar Philippines bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kan gidan yarin.

Jami'an tsaron Philippines na farautar wadanda suka tsere daga gidan yarin kasar
Jami'an tsaron Philippines na farautar wadanda suka tsere daga gidan yarin kasar REUTERS/Erik De Castro
Talla

Lamarin dai ya faru ne a gidan kurkukun Kidapawan da ke yammacin garin Davao wanda shi ne fadar gwamnatin lardin Mindanao.

Hukumomin kasar na zargin cewa, maharan na da alaka da kungiyoyin ‘yan aware na masu kishin muslunci, yayin da aka shafe sa’oi biyu suna harbe-barben bindigar.

Ana dai zargin an kaddamar da harin ne da nufin ceto ‘yan tawaye masu kishin Islama da ke garkame a gidan yarin.

Tuni dai jami’an ‘yan sanda da sojoji suka fara farautar wadanda suka yi nasarar tserewa daga kurkukun, in da kawo yanzu suka kama mutane shida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.