Isa ga babban shafi
Iran

Tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hachémi Rafsandjani ya rasu...

Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hachémi Rafsandjani, rasuwa daya daga cikin wadanda suka assasa jamhuriyar musulunci ta Iran a 1979.

Tsohon shugaban kasar Iran Marigayi Akbar Hachémi Rafsandjani
Tsohon shugaban kasar Iran Marigayi Akbar Hachémi Rafsandjani 路透社
Talla

Rafsandjani dan shekaru 82 a duniya, ya rasu ne sakamakon tsayawar bugun zuciya a asibitin Shohadaa da ke arewacin birnin Téhéran.

A lokacin rayuwarsa dai Rafsandjani, mai ra’ayin rikau ne, ya kuma shugabanci Iran daga shekarar 1989 zuwa1997, tare da gudanar da aiki mai wahalar gaske na sake gina kasar, bayan kawo karshen yakin shekaru 8 da ta gwabza da makwabciyarta kasar Irak (1980-1988). Ya kuma aiwatar da siyasar sassauci da kasashen yammaci.

A cikin jawabin da ya gabata ta kafafen Rediyo da Talabijin din kasar, jagoran juyin juya halin musuluncin kasar ta Iran ayatollah Ali Khamenei ya yaba wa marigayin da ya danganta a matsayin abokin gwagwarmaya, duk kuwa da banbancin ra’ayin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.