Isa ga babban shafi
Yemen

Yawan sojin da suka mutu a birnin Aden na Yemen ya karu

Kungiyar IS ta yi ikirarin kai harin kunar bakin waken da yayi sanadin mutuwar sojin kasar Yemen, a cibiyarsu da ke al-Solban a birnin Aden. 

Cibiyar sojin Yemen da ke al-Sawlaba a birnin Aden da aka kai harin kunar bakin wake
Cibiyar sojin Yemen da ke al-Sawlaba a birnin Aden da aka kai harin kunar bakin wake
Talla

A halin da ake ciki dai yawan sojin da suka rasa rayukansu a harin ya karu zuwa 49 daga 30 kamar yadda aka rawaito da safiyar yau.

Sati guda kenan da kungiyar ta IS ta kai irin wannan hari a kudancin birnin na Aden inda ta kashe sojin kasar akalla 50.

Wani dan kunar bakin wake ne ya halaka sojin kasar a cibiyar tasu a lokacin da ya tada bam din dake jikinsa.

Kawo yanzu dai sama da mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu a Yemen da ke fama da hare haren kungiyar IS a gefe guda kuma ga jagorantar barin wuta da Saudiya ke yi kan mayakan Houthi da ke da karfi a birnin Sanaa.

A yanzu Aden shi ne babban birnin kasar Yemen na wucin gadi, da gwamnatin kasar da ta samu amincewar kasashen Duniya, kuma ta ke gudun hijira a Saudiyya ke daukarsa a matsayin fadarta.

Har yanzu dai gwamnatin Yemen na kokarin ganin ta mallaki cikakken ikon birnin, wanda har yanzu, yake fuskantar hare-hare.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.