Isa ga babban shafi
Yemen

Mutanen da aka kashe a Yemen sun zarce 7,000

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce a cikin watanni 20 da aka kwashe ana yaki a kasar Yemen mutane sama da 7,000 aka kashe, yayin da aka raunana wasu kusan 37,000.

Dubban mutane ke bukatar taimako a Yemen
Dubban mutane ke bukatar taimako a Yemen STRINGER / AFP
Talla

Adadin mutane sama da 7,070 aka kashe tare da raunana 36,818 daga soma yakin a Yemen zuwa ranar 25 ga watan Oktoba.

Rahotan hukumar ya ce yanzu haka mutane miliyan 21 ke cikin mawuyacin hali na abin da zasu ci da kuma kula da lafiyar su a kasar.

WHO ta ce kimanin mutane Miliyan 2.1 rikicin na Yemen ya raba da gidajensu

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Ismail Ould Cheikh Ahmed ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ba za a lamunce da shi ba, wanda ya zama dole a kawo karshensa.

Tun a watan Maris na 2015 Yemen ake yaki a Yemen inda ‘Yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran ke fada da dakarun gwamnati da ke samun taimakon Saudiya da kawayenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.