Fada ya ritsa da mutane 200,000 a Yemen
Majiyar Sojin kasar Yemen tace akalla mutane 40 suka mutu a fafatwar da akayi tsakanin Yan Tawayen Huthi da dakarun dake goyan bayan gwamnatin kasar, a garin Taez dake kudu maso yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Kakakin sojin kasar Kanar Sadiq al-Hassani yace daga cikin mutanen da aka kasha, 27 ‘yan tawayen Huthi ne, kana 13 daga ciki sojojin gwamnati.
Har yanzu ana ci gaba da fafatawa tun bayan katsewar tattaunawar zaman lafiyar da akayi a kasar Kuwait.
Sama da fararen hula 200,000 ne fada ya ritsa da su a garin Taiz da ke tsakanin babban birnin kasar Yemen Sanaa da kuma birnin Aden.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu