Fada ya sake barkewa a Yemen bayan tsagaita wuta
Fada ya sake barkewa a Yemen duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta soma aiki a yau Assabar inda Rahotanni suka ce ‘Yan tawaye sun gwabza fada da dakarun gwamnati a garin Taez da ke kudu maso yammacin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majiyoyin tsaro da na lafiya sun ce ‘Yan tawayen Huthi sun harba makamin roka inda fararen hula uku suka mutu yayin da kuma aka kashe ‘Yan tawaye hudu a wani fada da suka gwabza da dakarun gwamnati kusa da garin na Taez.
Amurka ce dai ta jagoranci amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 48 da nufin bude kofar hawa teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da ya lakume rayukan dubban mutane.
Saudiya da kawayenta da ke taimakawa dakarun gwamnatin Yemen akan ‘Yan tawayen Huthi ‘Yan Shi’a ne suka sanar da amincewa da yarjejeniyar wacce kuma rahotanni suka ce ta soma aiki da safiyar Assabar.
An dai dade bangaren gwamnatin Yemen da Saudiya ke mara baya na yin watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu