Isa ga babban shafi
Yemen

An tsaigata buda wuta a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da tsagaita buda wuta a Yemen na Sa’o’I 72, kuma ana iya tsawaita yarjejeniyar da za ta soma aiki daga ranar Alhamis.

An tsaigata wuta na sa'o'i 72 a Yemen
An tsaigata wuta na sa'o'i 72 a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Majalisar ta sanar da hakan ne bayan Shugaban kasar ta Yemen, Abderabbo Mansour Hadi, ya amince a tsaigata wuta a jiya litinni, kwana guda bayan kiran da kasashen duniya suka yi kan wannan bukata.

Jakadan Majalisar na musamman a Yemen, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ce ya tuntubi mayakan Huthi domin amincewa da wannan bukata.

Kasashen Amurka da Britaniya da jakadan zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya a Yemen, sun bukaci bangarori da ke yaki da junan da su gaggauta tsaigata wuta, don neman hanyar kawo karshan yakin basasa a Yemen.

Rikicin kasar Yemen da Saudiya ke taka rawa ya lakume rayuka 6,900 da jikkata sama da 35,000, bayan miliyoyi da ya tilastawa gudun hijira tun daga watan Maris din shekarar da ta gabata a cewa Majalisar Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.