Isa ga babban shafi
Israel

Al’ummar Isra’ila na yi wa Shimon Perez bankwanan karshe

A yau alhamis an gabatar da akwatin da ke dauke da gawar tsohon Firaminista kuma tsohon shugaban Isra’ila Shimon Peres a gaban ginin majalisar dokokin kasar domin bai wa jama’a damar yi ma ta bankwanan karshe.

Al’ummar Isra’ila na yi wa Shimon Perez bankwanan karshe.
Al’ummar Isra’ila na yi wa Shimon Perez bankwanan karshe. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Daga wannan alhamis an sauko da tutocin kasar ta Isra’aila a ko’ina cikin duniya har na tsawon kwanaki kafin daga bisani a yai ma ta jana’iza tare da halartar shugabannin kasashen duniya da dama cikin har da Barack Obama da kuma shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas.

Shimon Peres, wanda ya rike mukamin Firaministan Israila sau biyu da shugaban kasa sau guda, ya kuma jagoranci tattaunawar zaman lafiya da Falasdinawa, ya kuma rasu ne yana da shekaru 93 sakamakon bugun zuciyar da ya samu a ranar litinin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.