Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta koka bisa halin da fararen hula ke ciki a Syria

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syrian Staffan de Mistura ya ce yakin da ake gwabzawa a kasar shi ne mafi muni da ya shafi fararen hula, tun bayan yakin duniya na biyu.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura tare da Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura tare da Sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry REUTERS/Darren Ornitz
Talla

Mistura ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan kokarin Majalisar Dinkin Duniya ta ke yi na kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Ya ce ba shakkah kasar Syrian ta sake fadawa cikin kazamin rikici, kuma hakan koma baya ne ga kokarin da ake yi na kawo karshen tashin hankalin da kasar ke fuskanta fiye da she karu biyar.

De Mistura ya kara da cewa bai taba ganin yakin da ya kunshi bangarori da dama da ke fada da juna ba kamar yakin na Syria.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.