Isa ga babban shafi
Saudiya

Sabuwar barazana ga gwamnatin Saudiya

Da ga marigayin madugun Kungiyar Al-Qaeda Osama Bin Laden, Hamza Bin Laden ya roki ‘yan kasar Saudiya da su yi dukkan mai yiwuwa domin kawar da gidan sarautar kasar saboda jama’a su ‘yantu daga hannun Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama tare da Sarkin Saudiya Salman
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Sarkin Saudiya Salman REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Hamza Bin Laden mai shekaru 23 cikin wata sanarwa daya fitar ya nemi matasan kasar Saudiya su shiga Kungiyar Al-Qa’ida reshen kasar Yemen domin sanin dabarun da zasu bi don kawo karshen gwamnati mai ci.

Kungiyar Al-Qaeda reshen Yemen wadda Amurka ta bayyana cewa tana da hatsarin gaske, tun shekara ta 2009 ta hade reshen Al-Qaeda dake Saudiyya.

Marigayi Osama Bin Laden dan kasar Saudiyya ne amma kuma tushen sa kasar Yemen.

A shekara ta 2011 sojan Amurka suka kutsa kai kasar Pakistan suka kashe Osama Bin Laden wanda suka kwashe kusan shekaru 10 suna farautar sa.

Tun a shekara ta 1994 Hukumomin Saudiyya suka kwace izinin zama dan kasar Saudiya daga hannun Marigayi Osama Bin aden a lokacin da ya furta la’antar gidan sarautar Saudiya da Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.