Isa ga babban shafi
IRAN

Masu ra’ayin canji sunyi nasara a zaben Iran

Jam ‘iyyar masu sassaunci ra’ayi ta shugaban kasar Iran Hassan Rouhani na gab da lashe zaben Majalisar dokokin kasar da aka gudanar a makon jiya bayan lashe kab kujerun majalissar dokokin kasar 30 da ke babban birnin kasar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani REUTERS/President.ir
Talla

Sakamakon farko na zaben da ake kallo a matsayin zakaran gwajin dafi ga shugaba Hassan Rouhanni, ya bayyana cewa Jam’iyyar sa ke kan gaba a yawan Kuri’u, bayan lashe sama da rabin kujeru 290 da ake da ita a majalissar.

Nasara wannan zabe, zai baiwa Rouhani damar gudanar da sauye-sauyensa na cikin gida, da sha’anin Siyasa kasar da fanin tattalin arziki.

Zaben dai shi ne na farko da kasar ta gudanar, tun bayan kulla yarjejeniya da manyan kasashen duniya kan shirinta na Nukiliya, abinda ya sa aka janye mata takunkuman karayar tattalin arziki.

Rahotanni sunce jam’iyyar Rouhani nada yawan kujeru 135 kawo yanzu cikin 260, yayin da jam’iyyar Conservative ta masu ra’ayi rikau da tsohon kakakin majalisar kasar Gholam ali-Hada Adel ke jagoranta ke da kujeru 38, sai sauran jam’iyyun dake da 30.

Sai dai har yanzu ba a kammala fitar da takaimaiman mai nasara a zaben ba, kuma akwai wasu kuri’u da aka gagara tantacewa. Kuma da yiwuwar aje ga zagaye na 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.