Isa ga babban shafi
Iran

Haddad Adel ya fice daga takarar zaben shugaban kasa a Iran

Daya daga cikin ‘Yan takarar neman mukamin shugabancin kasar Iran a bangaren masu tsatsauran ra’ayi Gholam Ali Haddad ya janye daga takarar neman wannan mukami. Gholan Ali Haddad wanda tsohon shugaban Majalisar dokokin kasar ta Iran ne, ya sanar da daukar wannan mataki ne a ranar litinin, inda ya bukaci magoya bayansa da su jefa kuri’unsu ga sauran ‘yan takara da ke da ra’ayi irin na shi.

'Yan takarar zaben shugaban kasar Iran
'Yan takarar zaben shugaban kasar Iran
Talla

A ranar juma’a mai zuwa ne za a gudanar da wanna zabe na shugabancin kasar Iran, inda mutane fiye da Milyan biyar suka cancanci jefa kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.