Isa ga babban shafi
Iran

Dan takarar masu sassaucin ra'ayi ne ke sahun gaban zaben Iran

Sakamakon zaben farko a Iran na nuni da cewa dan takara Hassan Rowhani da ake kallo a matsayin wanda ke samun goyon bayan samu sassaucin ra’ayi, shi ke kan gaba da yawan kuri’u kashi 49.87 bisa dari a sakamakon kuri’u kashi 10 da aka kada a zaben shugaban kasa.

Wata rumfar zabe a Iran
Wata rumfar zabe a Iran REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

Ma’aikatar cikin gidan Iran ta ce kuri’un da Rawhani ya samu sun ninka wanda ke bi masa a yawan kuri’u a zaben. Sai dai kuma dan takarar yana bukatar karin kuri’u domin kaucewa shiga zagaye na biyu a ranar 21 ga Yuni.

A tsarin zaben Iran dai dole sai dan takara ya lashe kashi 50 na kuri’un da aka kada kafin ya lashe zaben, idan kuma dan takara ya kasa samun kuri’un, to dole sai an shiga zagaye na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.