Isa ga babban shafi
Syria

ISIS ta saki fararen hulan da ta yi garkuwa da su a Syria

Kungiyar ISIS mai ikirarin jihadi ta saki fararen hula 270 daga cikin sama da 400 da ta sace a lokacin da ta kai farmaki a birnin Deir Ezzor da ke gabashin kasar Syria a karshen makon da ya gabata.

Kungiyar ISIS na ci gaba da tayar da kayar baya a kasar Syria
Kungiyar ISIS na ci gaba da tayar da kayar baya a kasar Syria
Talla

Shugaban kungiyar da ke sa ido kan hakkin bil adama a Syria, Rami Abdel Rahman ya ce, a jiya talata ne aka saki mutanen wadanda suka hada da mata da kananan yara ‘yan kasa da shekaru 14 har ma da tsofaffi.

Abdel Rahman ya ce, ISIS ta saki mutanen bayan ta yi musu jerin tambayoyi domin gano irin alakarsu da sojojin gwamnatin Syria.

An bada tabbacin cewa mutanen ba za su koma garin Deir Ezzor da zama ba,yayin da za a nema musu wuri a wasu sassa na yankin kamar yadda Abdel Rahman ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Yanzu haka dai kungiyar ta ISIS na ci gaba da yin garkuwa da mutane 130 yawancin su matasa kuma ana kyautata zaton tana can tana musu tambayoyi.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai kungiyar ta kai farmaki a garin, inda mayakanta suka tarwatsa kan su a harin na kunar bakin wake, kuma  yanzu haka tana rike da kashi 60 cikin 100 na birnin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.