Isa ga babban shafi
Saudiya-Iran

Saudiya ta katse hulda da Iran

Kasar Saudi Arabia ta katse huldar diflomasiya tsakaninta da Iran bayan wasu sun kona ofishin Jakadancin Saudiya a Tehran a lokacin da suke zanga-zangar adawa da kisan Malamin Shi’a Sheikh Nimr al Nimr.

An yi zanga-zangar adawa da kisan al-Nimr a Iran
An yi zanga-zangar adawa da kisan al-Nimr a Iran REUTERS/Raheb Homavandi/TIMA ATTENTION EDITORS - THIS IMAGE WAS
Talla

Ministan harkokin wajen Saudi Adel al Jubeir ne ya bayyana matsayin kasar tare da ba Jami’an diflomasiyar Iran wa’adin sa’oi 48 su fice daga Saudiya.

A ranar Asabar ne wasu matasa suka kai hari Ofishin jekadancin Saudiya a Tehran da wani karamin ofishinta a Mashhad.

Saudiya ta zartar da hukuncin kisa akan Nimr bayan kama shi da laifin tunzura jama’a domin adawa da gwamnati a 2011.

A martanin da ta mayar, Iran tace katse hulda da ita ba zai karkatar da hankalin duniya ba akan kuskuren Saudiya na kisan Malamin na shi’a.

Kasashen Amurka da Faransa da Jamus sun bukaci manyan kasashen na gabas ta tsakiya su bi hanyoyin lalama domin warware sabanin da ke tsakaninsu.

Shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah ya bayyana gidan Sarautar Saudiya a matsayin wanda ke neman haifar da tashin hankali tsakanin mabiya Shi’a da Sunni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.