Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kashe mutane 5 a Kabul

Jami’an tsaron Afghanistan sun yi nasarar murkushe mayakan Taliban da suka kaddamar da hare hare a kusa da ofishin jekadancin kasashen waje a Kabul, kamar yadda Ministan cikin gida Sediq Sediqqi ya sanar a shafin shi na Twitter.

Taliban ta kashe 'Yan sanda 4 a harin da ta kai kusa ofishin jekadancin Spain a Kabul
Taliban ta kashe 'Yan sanda 4 a harin da ta kai kusa ofishin jekadancin Spain a Kabul REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Akalla mutune biyar aka kashe a hare haren da mayakan Taliban sun kai yau Assabar a kusa da ginin ofishin jekadancin kasar Spain a Kabul. Akwai ‘Yan sanda 4 cikin wadanda suka mutu.

An shafe sa’o’I jami’an tsaron Afghanistan na musayar albarussai da ‘Yan Taliban.

Wannan kuma na zuwa ne sa’o’I bayan shugaban Afghanistan Ashraf Gani ya bayyana kwarin guiwarsa na komawa teburin tattaunawa da Taliban nan da makwanni biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.