Isa ga babban shafi
Malaysia

Ana zanga zanagar adawa da Najib Razak a kasar Malaysia

Yau wasu Lahadi, ‘yan kasar Malaysia suka koma kan titunan birnin Kuala Lumpur, inda suke zanga zangar neman Fraiminista Najib Razak yayi murabus.

Fraiministan kasar Malaysia, Najib Razak
Fraiministan kasar Malaysia, Najib Razak REUTERS
Talla

Dama jiya Asabar wasu dubun dubatar ‘yan kasar suka hana ruwa gudu a birnin, lokacin da suka gudanar da wata zanga zangar lumana, duk da cewa ‘yan sanda sun bayyana cewa matakin da cewa ya saba doka.
Zanga zangar kwanaki biyun, na matsayin wadanda suka fi samun karbuwa a kasar ta Malaysia cikin shekaru da dama, inda jama’a suka sanya riguna masu ruwan dorawa, suka kwana a dandalin ‘yanci na birnin Bangkok.
Fraiminista Najib Razak ya shiga tsaka mai wuya ne bayan da wata jaridar kasar Amurka ta bayyana cewa an shigar da wasu kudaden gwamnati a asusun ajiyar sa na banki.
Sai dai kuma Fraiministan ya bayyana zargin a matsayin bita da kullin siyasa.
Yayinda ake wasu kananan zanga zanga a sauran yankunan kasar, ‘yan sanda sun bayyana kame akalla mutane 12 dake cikin zanga zangar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.