Isa ga babban shafi
Malaysia

Kotu ta yankewa mutane hudu hukuncin kisa a Malaysia

Wata kotun kasar Malaysia, ta yankewa wasu mutane hudu hukuncin kisa, ta hanyar rataya, bayan da ta same su da laifin kashe wata ‘yar kasuwa da abokan huldar ta su uku.

Wasu jami'an tsaron kasar Malaysia
Wasu jami'an tsaron kasar Malaysia
Talla

Mutanen da suka hada da lauya daya, sun kashe Sosilawati Lawiya, mai shekaru 47, direban ta, lauyan ta da wani ma’aikacin banki a shekarar 2010, lamarin da ya girgiza jama’a, tare da daukar hankulan kafafen yada labarun kasar.

An bayar da sanarwar bacewar mutanen a lokacin da suka je cinikin wani filin lauyan da dan uwan shi a gonarsu.

‘Yan sanda sun ce an kone gawarwakin mutanen, aka kuma zuba burbushin su a kogi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.