Sakacin Jami’an gwamnati ya baiwa ISIL nasara iko da Mosul
Wani bincike ya nuna cewa sakacin manyan jami’an gwamnati Iraqi ne yasa mayakan ISIL suka iya kwace birnin Mosul a bara, ganin yadda suka nuna halin ko in kula bayan sun samu mahinman rahotanni da ke gargadin cewa mayakan na kokarin kai hare hare a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Rahotan ya bayyana sunan manyan jami’an gwamnati da cikin su har da mataimakin shugaban kasar Nuri al-Maliki da ke da hannu a nuna halin ko in kula akan tsaron kasar.
Rahotan ya kara da cewa duk manyan jami’an gwamnatin na sane mayakan ISIL na shirin kai hare hare a cikin kasar kuma sun gagara daukar matakai har sai dai mayakan suka yi nasarar kwace babban birnin na Mosul.
Sakamakon hakan ne dakarun gwamnati suka tafka kura-kurai a yayin fafatawar su da mayakan har suka kai ga nasarar karbe birnin.
Rahotan dai ya zargi al-Maliki da kasa kafa runduna soji mai karfi da ka iya fuskantar duk wata yan ta’ada a kasar bayan karbe birnin Mosul da yankin Nineveh, yanzu mayakan sun nufi kudancin kasar da niyar karbe ikon yankin baki daya.
Tuni dai mataimakin shugaban kasar Nurul al-Maliki ya yi watsi da wannan rahoton inda ya ce bashi da wani amfani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu