Isa ga babban shafi
Iraqi

Majallisar dokokin Iraqi ta bukaci a gurfanar da tsohon Firiministan Kasar

‘Yan majalissun dokokin Iraqi sun zargi tsohon Frimiya kasar Nuri-al-Maliki da wasu mutane 35 da alhakin faduwar Birnin Mosul na biyu mafi muhimmaci a kasar hannu Mayakan Jihadi a shekarar da ta shude.

Tsohon firiminista Nuri al-Maliki yayin halarta shi wani zaman majalisar
Tsohon firiminista Nuri al-Maliki yayin halarta shi wani zaman majalisar Reuters/路透社
Talla

Kwamitin Bincike a majalisar karkashin jagorancin Abdulrahim al-Shammari sun ce Maliki wanda shine Firiya Minista kasar daga shekarar 2006 zuwa 2014 na daga cikin wadanda suka taka rawa aka rasa yankin Mosul.

Bayan Maliki, akwai wasu manyan Jami'an gwamnatin Iraqi da majalissar ta ce suma na taimakawa Mayakan Jihadi duk da dai majalisar ba ta ambato sunayen su.

Tuni dai kakakin majalisar Salim al-Juburi ya ce za a aika rahoton gaban masu shigar da kara domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Mayakan ISIL dai na yawaita kaddamar da hare-hare a Iraqi tare da kwace ikon yankunan kasar da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.