Isa ga babban shafi
Syria-Iraq

An yi wa IS luguden wuta a Iraqi

Jiragen Yakin Amurka da na Kawancen kasashen da ke yaki da mayakan ISIS a kasar Iraqi da Syria sun ce sun kai jerin hare haren sama 29 a karshen mako, inda suka lalata kamfanin hada makamai da wasu sassan da mayakan suke.

Sojojin Iraqi da ke fada da mayakan ISIL
Sojojin Iraqi da ke fada da mayakan ISIL REUTERS/Stringer
Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar tace sun kai hare hare 21 a garuruwan Makhmur da Ramadi da Bayji da ke Iraqi da kuma 8 a Syria cikin su har da biyar da aka kai Al Haska.

Wannan na zuwa ne a yayin da Kungiyar Mayakan ISIL da ke da’awar Jihadi ta bayyana daukar alhakin harin bama bamai Baquba da ke kasar Iraqi wadanda suka kashe mutane 42.

Bam na farko ya tashi ne kusa da kasuwa inda ya hallaka mutane 35, ya kuma raunana wasu kusan 70.

Bam na biyu ya tashi wajen binciken ababan hawa inda ya kashae mutane 7.

Mayakan ISIL dai sun kasha mutane da dama tare da tursasawa daruruwa tserewa gidajensu a Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.