Isa ga babban shafi
Iraqi

Harin bom ya kashe mutane 60 a Iraqi

Akalla mutane 33 suka mutu a wani mummunan harin bom da aka kai a mota a-kori-kura cikin kasuwar garin Sadr da ke arewa da Bagadaza babban birnin kasar Iraqi.

Akalla mutane 60 suka mutu a wani mummunan harin bom da aka kai a mota a-kori-kura cikin kasuwar garin Sadr
Akalla mutane 60 suka mutu a wani mummunan harin bom da aka kai a mota a-kori-kura cikin kasuwar garin Sadr REUTERS/Wissm Al- Okili
Talla

Motar ta kutsa ne cikin kasuwa da safe kafin bom din ya tarwatse a inda ake sayar da kayan miya. Harin kuma ya raunana akalla mutane 200, kamar yadda mahukuntan Iraqi suka tabbatar.

Harin ya kashe Dawakin da ‘Yan kasuwa ke amfani da su domin dakon kayan miya zuwa kasuwa.

Yawancin mazauna yankin garin Sadr dai mabiya akidar Shi’a ne, kuma zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai harin. Amma mayakan IS da ke da’awar Jihadi sun dade suna kai wa mabiya Shi’a hari a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.