Isa ga babban shafi
India

Mutane 33 sun mutu a Mumbai bayan sun kwankwadi barasa mai guba

‘Yan sanda a kasar India sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 33 a birnin Mumbai bayan sun kwankwadi barasa mai guba da ake hadawa a cikin kasar. ‘Yan sandan sun ce akwai  wasu mutane 9 cikin wadanda suka kwankwadi barasar da ke cikin mawuyacin hali.

'Yan uwan wadanda suka mutu na jimami a India
'Yan uwan wadanda suka mutu na jimami a India © Reuters/ Rupak De Chowdhuri
Talla

‘Yan sandan sun ce nan take mutanen suka kamu da rashin lafiya bayan sun kwankwadi barasar, kuma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa, domin yanzu haka mutane 9 na can mutu-kwakwai rai-kwakwai.

Rundunar ‘Yan sandan Mumbai tace ta kama mutane uku da ake zargi sun hada barasar kuma suna kan bincike.

An dade dai ana samun mutuwar mutane a India ta hanyar kwankwadar Barasa da ake sayarwa cikin karamar kwalba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.