Isa ga babban shafi
india

Mutane 170 sun mutu sanadiyar kwankwadar barasa a India

Jami’an tsaro a kasar India sun tabbtar da mutuwar mutane 170 sanadiyar kwankwadar wata barasa mai dauke da guba a gabacin India a yankunan Parganis da ke karkashin Jahar Bengal. Wadanda al’amarin ya shafa sun fito ne daga kauyuka 10 da ke makwabtaka da kan iyaka da Bangladesh.

mutane dauke da wadanda suka mutu sanadiyar kwankwadar barasa mai guba a Indiya
mutane dauke da wadanda suka mutu sanadiyar kwankwadar barasa mai guba a Indiya REUTERS
Talla

‘Yan Sanda sun ce yanzu haka wasu sama da 100 na asibiti ana kula da su, kuma tuni suka cafke mutane hudu da ke da hannu wajen hada barasar.

Ko a makon jiya, sai a Jihar Gujurat ta amince da dokar hukuncin kisa kan masu hada irin wannan barasa, ganin yadda suke hallaka jama’a.

Masana kiyon lafiya sun ce idan har mutum ya kwankwadi irin wannan barasar yakan iya makancewa tare da bata masa koda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.