Isa ga babban shafi
Libya

Mutane 51 sun mutu a Libya sakamakon shan Barasa mai dauke da guba

Ma’aikatar Lafiya a Libya, ta ce akalla mutane 51 suka mutu sakamon kwankadar ruwan giya mai dauke da guba a birnin Tripoli. An kuma bayyana wasu mutane 378 suka kamu da rashin lafiya.

Gawar mutanen India bayan sun sha barasa mai dauke da Guba
Gawar mutanen India bayan sun sha barasa mai dauke da Guba
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar, Hussein al-Ameri, yace an kaddamar da bincike domin gano abinda ya kashe mutanen a cikin giyar.

Wani jami’in asibiti, Youssef akl-Wafi, yace binciken farko ya nuna cewar an sanya guba ne a giyar.

A tsarin dokar kasar libya, haramun ne a sha giya ko sayar da ita, amma kuma ana sayar da giyan a bayan fage.

Yanzu haka an kafa dokar t abaci a asibitocin birnin Tripoli

Rahotanni sun ce an samar da giyan ne a cikin kasar Libya da ake kira da sunan Bokha. Amma ana fataucin giya ne zuwa Libya daga kasashen Tunisia da Algeria da kuma Malta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.