Isa ga babban shafi
MDD-Yemen

Ban ki-moon ya bukaci a gaggauta kawo karshan rikicin Yemen

Sakataren Majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarorin da ke rikici a Yemen su gaggauta amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a yayin da ake tattauna yadda za a shawo kan rikicin kasar a Geneva.Kiran Ban Ki-moon na zuwa ne a yayin da Saudiya da kawayenta ke ci gaba da luguden wuta akan ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi’a a Yemen.

Sakatare Janar na MDD Ban ki moon
Sakatare Janar na MDD Ban ki moon REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

An dade dai shugabannin kasashen duniya na kokarin ganin sun shiga tsakani domin kawo karshen rikicin Yemen, musamman saboda barazanar yaduwar kungiyoyi ma su tayar da kayar baya irinsu al-Qaeda a gabas ta tsakiya.

Yanzu haka kuma an bude zaman sasanta rikicin Yemen a Geneva a jiya Litinin.

Kuma sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarorin da ke rikici su gaggauta amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta, domin shigar da kayan jin kai da dimbin al’ummar kasar da rikici ya dadaita.

Lura da soma azumin Watan Ramadan, Ban yana ganin ya dace a tsagaita wuta.

MDD ta ce kusan kashi 80 na al’ummar kasar Miliyan 20, na bukatar tallafin abinci . ya yin da rikicin kasar ya yi sanadin mutuwar mutane 2,600, yawancinsu fararen hula.

Rikicin kuma ya shafi ‘Yan tawayen Huthi mabiya shi’a wadanda Iran ke marawa baya da kuma dakarun gwamnatin Abedrabbo Mansour Hadi da kasashen duniya ke marawa baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.