Isa ga babban shafi
Yemen

Yan tawayen Yemen sun kama wani gari kusa da iyakar Saudiya

Mayakan kungiyar Yen shi'ar kasar Yemen sun yi nasarar kama wani babban gari a kusa da kan iyakar yankin arewacin kasar da kasar Saudiya, duk da cewa MDD na shirin gudanar da wani zaman taron neman zaman lafiya a kasar.

Wani mayaki na yan shi'ar kasar Yemen a kan titin birnin Aden, a ranar  9 da watan mayu  2015.
Wani mayaki na yan shi'ar kasar Yemen a kan titin birnin Aden, a ranar 9 da watan mayu 2015. REUTERS/Stringer
Talla

‘Yan tawayen Hutin yan shi’ar kasar Yemen sun yi nasarar kama wani babban gari dake yankin arewacin kasar ta Yemen gab da kan iyakar kasar da kasar saudiya, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar,

Wannan kuma na zuwa ne ana sauran kwana guda,  a shiga tattaunawar neman zaman lafiya a karkashin jagorancin MDD a birnin Geneve na kasar Switzerland.

Kakkakin MDD Ahmad Fawzi ya ce, yanzu haka dai suna jiran zuwan wakilan bangarorin biyu a birnin na Geneve domin shiga tattaunawar a gobe litanin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.