Isa ga babban shafi
Somalia-Yemen

Mutanen Yemen 7,000 sun tsallaka zuwa Somalia

Majalisar Dinkin Duniya tace Kimanin ‘Yan gudun hijira 7,000 ne suka tsere daga Yemen zuwa Somalia tun lokacin da Saudiya da kawayenta suka kaddamar da farmaki akan ‘Yan tawayen Huthi mabiya Shi ‘a a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace Kimanin ‘Yan gudun hijira 7,000 ne suka tsere daga Yemen zuwa Somalia  saboda rikicin kasar
Majalisar Dinkin Duniya tace Kimanin ‘Yan gudun hijira 7,000 ne suka tsere daga Yemen zuwa Somalia saboda rikicin kasar REUTERS/Mohamed al-Sayaghi TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Majalisar Dinkin Duniya tace akwai bukatar kai daukin agajin gaggawa zuwa Somalia mai fama da rikicin Al Shabaab bayan kwararar mutanen na Yemen a cikin kasar.

‘Yan gudun hijirar na Yemen dai sun shiga cikin jerin mutanen Somalia Miliyan uku da ke fama da matsalar karancin abinci.

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Somalia Nicolas Kay ya yi kira ga Kwamitin tsaro ya gaggauta daukar matakin da ya dace tun kafin mayakan Al Shabaab na Somalia su fara samun goyon bayan masu tsatstsauran ra’ayi a Yemen.

Jami’in ya ce zasu ci gaba da sa ido tare da daukar matakan gaggawa na dakile duk wata hanya da mayakan Al Shabaab za su hada kai da mayakan Yemen.

Matsalar kwararan Mutanen Yemen ya kara haifar da matsaloli ga dimbin jama’ar d Somalia da ke neman agajin gaggawa.

Tuni dai Firaministan Somala Omar Abdirashin Ali Sharmake ya yi gargadi cewa mayakan Al Qaeda na Yemen na iya rikidewa cikin ‘Yan gudun hijira don su shigo Somalia.

Gwamnatin kasar yanzu ta fara tantance mutanen Yemen da ke kwarara zuwa cikin Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.