Isa ga babban shafi
Gaza

Manoman Gaza sun fara shigar da kaya zuwa Isra’ila

Manoma a yankin Zirin Gaza sun fara shigar da kayan abinci zuwa ga yahudawan Isra’ila, wanda shi ne karon farko da mutanen na gaza suka shigar da kaya tun 2006 da Isra’ila ta killace mashigin Gaza. Wannan wani mataki ne na taimakawa manoman Gaza tare da biyan bukatun Yahudawa ga albarkun noma.

Gonar Tomatur a Deir El-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza
Gonar Tomatur a Deir El-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza REUTERS
Talla

Isra’ila ta dauki matakin ne domin biyan bukatun Yahudawa masu tsatstsauran ra’ayi da suke haramta wa kansu cin abincin da Yahudawa suka noma duk bayan shekara bakwai a kalandar Yahudawa.

A tsarin Isra’ila duk bayan shekaru bakwai Yahudawa masu zazzafan ra’ayi da ake kira Ultra-Orthodox na haramtawa kansu sayen kayan lambu da kayan marmari da Yahudawan Isra’ila suka noma.

Falasdinawa akalla sama da miliyan 1,8 ne suka dogara da noma, kuma gwamnatin Isra’ila ta haramta shigo da kaya a 2007 daga Gaza bayan Hamas ta karbe ikon yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.