Isa ga babban shafi
Isra'ila-Gaza

Isra’ila za ta fara shigo da kayan noma daga Gaza

Yahudawan Isra’ila masu zazzafan ra’ayi za su fara sayen kayayyakin amfani Gona daga hannun manoma a yankin gaza, wanda shi ne karon farko tsawon shekaru bakwai da suka gabata. Wannan wani mataki ne na taimakawa manoman Gaza tare da biyan bukatun Yahudawa ga albarkun noma.

Mutanen yankin Gaza
Mutanen yankin Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

A tsarin Isra’ila duk bayan shekaru bakwai Yahudawa masu zazzafan ra’ayi da ake kira Ultra-Orthodox na haramtawa kansu sayen kayan lambu da kayan marmari da Yahudawan Isra’ila suka noma.

Wannan ne kuma karon farko tun bayan shekarar ta 2007 da za a yi cinikin kayayyakin lambu tsakanin Isra’ila da Gaza, lamari da zai karfafa ci gaba tattalin arzikin albarkatun gona a Gaza.

Falasdinawa akalla sama da miliyan 1,8 ne suka dogara da noma, kuma gwamnatin Isra’ila ta haramta shigo da kaya a 2007 daga Gaza bayan Hamas ta karbe ikon yankin.

Isra’ila ta koma shigo da kayayyakin amfani gona daga kasashen yammaci ko yankin da ke gabar yamma da Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.